ABNA24 : Tun da fari, kungiyoyin na palasdinawa sun sanar da cewa za gudanar da taruka da jerin gwano da kuma jawabai a sassa daban-daban na Palasdinu domin raya ranar ta kasa da kuma nuna kin amincewa da yarjejeniyar kasashen larabawa da ‘yan sahayoniya.
A garin Khalil, Palasdinawan sun yi taro midanu shuhada’a, da Dawwar Ibn Rushdi. Sai kuma garin Tul-Karam da garin Jenin.
Garuruwan da aka yi taruka da jerin gwano sun hada Ramallah, da kuma Nablus.
Wata sanarwa ta kungiyoyin Palasdinawa ta kunshi bayyana ranar Juma’a mai zuwa a matsayin wacce za a daga bakaken tutoci domin yin tir da yarjejeniyar larabawan da yahudawa ‘yan mamaya.
342/